5 Yuni 2020 - 15:10
Takunkumin Da Amurka Ta Labta Wa China Kan Cin Zarafin Musulmi, Ya Fara Aiki

Sabon takunkumin da Amurka ta kakaba kan wasu manyan kamfanoni da cibiyoyin China kan zargin cin zarafin musulmi ya fara aiki.

(ABNA24.com) Bangarorin da Amurka ta kakaba wa takunkumin sun hada da kamfanonin fasahar China da kuma wasu manyan cibiyoyi guda tara.

Dukkansu Amurka na zarginsu da hannu a cin zarafi da azabtarwa kan Musulmi 'yan kabilar Uighur da sauran Musulmin kasar.

Saidai gwamnatin China na mai zargin Amurka ta tsoma baki a harkokin cikin gidanta game da lamuran tsirarun kabilu a yankin Xinjaiang.

Hakazalika kuma Amurkan ta sake sanya haramci a kan wasu kamfanoni China su guda 24 da ke samar wa dakarun kasar makamai.

342/